Acts 16

Timoti Ya Bi Bulus da Sila

1Bulus ya kai Derbe saʼan nan kuma zuwa Listira, inda wani almajiri mai suna Timoti yake da zama, wanda mahaifiyarsa Bayahudiya ce kuma mai bi ce, amma mahaifinsa Bahelene ne. 2ʼYanʼuwa a Listira da Ikoniyum sun yi magana mai kyau ƙwarai a kansa. 3Bulus ya so ya ɗauke shi a tafiyar, saboda haka ya yi masa kaciya, domin Yahudawan da suke da zama a wurin, don duk sun san cewa mahaifinsa Bahelene ne. 4Yayinda suke tafiya daga gari zuwa gari, suka dinga ba da shawarwarin da manzanni da dattawa a Urushalima suka zartar domin mutane su kiyaye. 5Saboda haka ikkilisiyoyi suka ginu cikin bangaskiya suka kuma yi girma suka yi ta ƙaruwa kowace rana.

Wahayin Bulus na Mutumin Makidoniya

6Bulus da abokan tafiyarsa suka zazzaga dukan yankin Firjiya da Galatiya, don Ruhu Mai Tsarki ya hana su yin waʼazi a lardin Asiya. 7Da suka isa kan iyakar Misiya, suka yi ƙoƙari su shiga Bitiniya, amma Ruhun Yesu bai yarda musu ba. 8Saboda haka suka ratsa Misiya suka zo Toruwas. 9Da dare Bulus ya ga wahayin wani mutumin Makidoniya yana tsaye yana roƙonsa cewa, “Ka zo Makidoniya ka taimake mu.” 10Bayan Bulus ya ga wahayin, muka shirya nan take mu tashi zuwa Makidoniya, mun tabbata cewa, Allah ya kira mu mu yi musu waʼazin bishara.

Tuban Lidiya a Filibbi

11Daga Toruwas muka tashi zuwa teku muka kuma shiga jirgin ruwa muka miƙe kai tsaye zuwa Samotiras, washegari kuma muka nufi Neyafolis. 12Daga can muka tafi Filibbi, wata babbar alkaryar Roma wadda kuma take babban birni a gundumar Makidoniya. Muka zauna a can kwanaki masu yawa.

13A Asabbaci, muka fita ƙofar birnin zuwa bakin kogi, inda muke tsammani za mu sami wurin yin adduʼa. Muka zauna muka fara yin wa matan da suka taru a can magana. 14Ɗaya daga cikin waɗanda suka saurare mu mace ce mai suna Lidiya, mai sayar da yardunan jan garura masu tsada daga birnin Tiyatira, mai yi wa Allah sujada. Ubangiji ya buɗe zuciyarta har ta karɓi saƙon Bulus. 15Da aka yi mata baftisma tare da iyalin gidanta, sai ta gayyace mu zuwa gidanta. Ta ce, “In kun amince ni mai bi ce cikin Ubangiji, sai ku zo ku sauka a gidana.” Sai ta kuwa rinjaye mu.

Bulus da Sila a Kurkuku

16Wata rana muna tafiya zuwa wurin yin adduʼa, sai muka sadu da wata baranya mai ruhun aljani mai duba. Takan samo wa mutanenta kuɗi da yawa-duban da take yi. 17Wannan yarinya kuwa ta bi Bulus da kuma sauranmu, tana ihu tana cewa, “Waɗannan mutane bayin Allah Mafi Ɗaukaka ne, suna sanar da ku hanyar ceto.” 18Ta yi ta faɗin haka har kwanaki masu yawa. A ƙarshe Bulus ya damu ƙwarai sai ya juya ya ce wa aljanin, “A cikin sunan Yesu na umarce ka, ka rabu da ita!” Nan take aljanin ya rabu da ita.

19Da iyayengijin baranyar suka ga hanyar samun kuɗinsu ta toshe, sai suka kama Bulus da Sila suka ja su zuwa cikin kasuwa don su fuskanci hukuma. 20Sai suka kawo su a gaban alƙalai suka ce, “Waɗannan Yahudawa ne, suna kuma birkitar mana da gari, 21ta wurin koyar da alʼadun da ba daidai ba ne mu Romawa mu karɓa ko mu aikata.”

22Sai taron suka fāɗa wa Bulus da Sila gaba ɗaya, alƙalan kuwa suka yi umarni a tuɓe su a kuma yi musu dūka. 23Bayan an yi musu bulala sosai, sai aka jefa su cikin kurkuku, aka umarci mai gadin kurkukun yǎ tsare su da kyau. 24Da karɓan irin umarnan nan, sai ya sa su can cikin ɗakin kurkuku na ciki-ciki, kuma ya ɗaura ƙafafunsu a turu.

25Wajen tsakar dare Bulus da Sila suna adduʼa suna rera waƙoƙi ga Allah, sauran ʼyan kurkuku kuwa suna sauraronsu. 26Ba zato ba tsammani sai aka yi wata babbar girgizar ƙasa har tushin ginin kurkukun ya jijjiga. Nan da nan sai duk ƙofofin kurkukun suka bubbuɗe, sarƙoƙin kowa kuma suka ɓaɓɓalle. 27Mai gadin kurkukun ya farka daga barci, saʼad da ya ga ƙofofin kurkukun a buɗe, sai ya zāre takobinsa yana shirin kashe kansa domin ya ɗauka ʼyan kurkukun sun gudu. 28Amma Bulus ya yi ihu, ya ce, “Kada ka yi wa kanka lahani! Dukanmu muna nan!”

29Mai gadin kurkukun ya kira a kawo fitilu, ya ruga ciki ya fāɗi yana rawan jiki a gaban Bulus da Sila. 30Sai ya fito da su waje ya kuma tambaye su ya ce, “Ranku yǎ daɗe, me zan yi domin in sami ceto?”

31Suka amsa suka ce, “Ka gaskata da Ubangiji Yesu, za ka sami ceto-kai da iyalinka.” 32Saʼan nan suka yi masa maganar Ubangiji shi da kuma dukan sauran da suke a gidansa. 33A wannan saʼa na daren, mai gadin kurkukun ya ɗauke su ya wanƙe musu raunukansu; nan take aka yi masa baftisma da dukan iyalinsa. 34Sai mai gadin kurkukun ya kawo su cikin gidansa ya ba su abinci; ya kuwa cika da murna don ya gaskata da Allah-shi da dukan iyalinsa.

35Da gari ya waye, sai alƙalan suka aika maʼaikatansu wajen mai gadin kurkukun da umarni cewa: “Ka saki mutanen nan.” 36Sai mai gadin kurkukun ya gaya wa Bulus cewa, “Alƙalai sun ba da umarni a sake ku kai da Sila. Yanzu sai ku tafi. Ku sauka lafiya.”

37Amma Bulus ya ce wa maʼaikatan: “Sun yi mana dūka a fili ba tare da shariʼa ba, ko da yake mu ʼyan ƙasar Roma ne, suka kuma jefa mu cikin kurkuku. Yanzu suna so su fitar da mu a ɓoye? Aʼa! Sai dai su zo da kansu su rako mu waje.”

38Sai maʼaikatan suka faɗa wa alƙalan wannan, da suka ji cewa Bulus da Sila Romawa ne, sai suka ji tsoro. 39Sai suka zo don su roƙe su, suka yi musu rakiya daga kurkukun, suna roƙonsu su bar birnin. 40Bayan Bulus da Sila suka fita daga kurkukun, sai suka tafi gidan Lidiya, inda suka sadu da ʼyanʼuwa suka kuma ƙarfafa su. Saʼan nan suka tafi.

Copyright information for HauSRK